Tarihin Manzon Allah S.A.W

By Bookshop
0
(0)
0 189
Free
In Stock
PDF File

GABATARWA

Da Sunan Allah Mai rahama Mai Jinkai, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad 19 (SAW) da iyalansa da zuriyarsa da sahabbansa da wadanda suka biye musu da kyawon aiki har zuwa ranar sakamako.

Wannan tarihi na wani littafi ne, wanda aka yi masa fassara zuwa harshen Hausa, mai suna kamar haka: ‚The Life of Muhammad (SAW),‛ wanda Dr. Muhammad Husain Haikal ya wallafa, kuma Sheikh Isma’il Raji A. AlFaruki ya fassarasa da harshen Turanci daga harshen Turanci a dab’i na takwas. Saboda haka Hajiya Daula Justice Muhammad Bello ta dauki nauyin fassara, kamar yadda mai karatu zai fahimci mafarin wannan fassara. Ni Is’hak Yunus Muhammad Tukur Almashgool Bauchi na fassara daga harshen Turanci zuwa harshen Hausa, ta re da yin wasu gyare-gyare a wasu bangarori da suka shafi tarihi. Musamman tarihin da Orientalists (mustashirikai) suka samar na karya dangane da rayuwar Muhammad (SAW) da abubuwa da suka shafi addinin Musulunci, Allah Ya kar~a mana wan nan aiki Ya sanya Aljanna ce makomarmu.

Bayan haka ina fatar jama’ar Musulmai za su amfana da wannan littafi mai muhimmanci, musamman masu magana da harshen Hausa. Saboda haka Hajiya Daula Justice Muhammad Bello, ta yi tunanin wannan aiki ne, saboda babu wani littafi na tarihin Manzon Allah (SAW) wanda ya ke da girma kuma mayalwaci kamar wannan wadda ta dauki nauyi wajen fassara shi zuwa harshen Hausa. Kuma shi mai littafin da wanda ya yi wa littafin fassara sun sami kansu wajen bin ra’ayin Orientalists musamman wajen kawo fassarar wasu ayoyi da wasu hadisai wadanda ba su inganta ba, wanda na yi iya kokari na wajen gyarawa tare da kawo hadisai da suka inganta game da wadan nan bangarori, ina rokon Allah SWT Ya gafarta mana kuskurenmu. Wannan littafi ya yalwata magana akan wasu bangarori na tarihi amma bai cika kawo labarin da aka sani cikin wananun litattafan tarihi ba, saboda haka mai karatu zai ga wasu yake-yake da Annabi (SAW) ya aiwatar, bai ambace su ba. Haka kuma siffofin Annabi (SAW) bai ambace su ba, amma na bayyana wasu daga cikinsu a takaice, kuma mai littafin ko mai fassara da harshen Turanci bai cika kawo in da ya ciro labari ba, don haka duk in da na ga haka, na kan ce: ban san in da mai littafi ya ciro wannan labari ba. Kuma na kanyi kokarin kawo abin da ya tabbata gwargwadon iko, saboda wannan fassara na yi shi ne cikin kwanaki arba’in daidai.

Daga karshe ina mika godiya ta musamman ga Hajiya Daula Justice Muhammad Bello wadda ta dauki nauyin fassarar wannan littafi, mai muhimmanci Allah Ya saka mata da alherinSa. Kuma ina mika godiya ta ga mata ta Malama Suwaiba Sa’id Muhammad Awwal saboda gudummuwar da 20 ta bayar wajen wannan aiki ta fuskar ha}uri da juriya. Kuma ina mi}a godiya ta ga Malam Sadik Isa Modibbo wanda ya ]auki ]awainiyar kaiwa da komowa wajen tabbatar da wannan aiki ya tabbata. Allah Ya sa ka mana da alherinSa.

No reviews found.

No comments found for this product. Be the first to comment!